Mataimakin Shugaban Kasa Sanata Kashim Shattima ya bukaci Kasar Saudiya ta mayar da aikin hidimar ciyar da alhazan Najeriya ga kasar domin magance korafe-korafen da alhazan ke yi a duk shekara da nufin kawo gyara a lokacin aikin Hajji mai zuwa na shekar 2024.
Shattima ya bukaci hakan ne a lokacin da hukumar kula da aikin Hajji ta Kasa NAHCON, karkashin jagorancin shugabanta Barista Zikrullah Kulle Hassan suka kaiwa mataimakin shugaban Kashim Shettima ziyara domin gabatar masa da rahoton yadda aka gudanar da aikin Hajjin shekarar 2023 da shirye-shiryen aikin Hajjin shekarar 2024.
Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da daraktan yada labarai da hulda da Jama’a na hukumar Musa Ubana Dawaki, ya aike ga manema labarai inda ya ce a ranar 20 ga watan Yuli na shekarar 2023, shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu, ya mayar da kula da harkokin hukamar karkashin kulawar ofishin mataimakin shugaban Kasa Kashim Shattima.
Bayan yabawa da yadda NAHCON ta gudanar da aikin Hajjin 2023 Shattima, ya ce mayar da harkokin ciyarwar karkashin hukumar jindadin alhazan jihohi zai taimaka wajen inganta dandanon abincin da zai dai-dai da wanda suke ci tare da kula da tsaftarsa yadda Alhazan zasu iya ci cikin kwanciyar hankali su kuma gudanar da ibadar aikin Hajjin cikin nutsuwa.
Kashim, ya kuma bukaci shugabancin hukumar karkashin Barista Zikirullah Hassan da su cigaba da wayar da kan alhazan Najeriya sharudai da hukunce- hukunce da ka’idojin aikin Hajji domin hakan zai kara taimakawa maniyyatan yadda zasu gudar da aikin Hajjin kamar yadda addinin muslinci ya tsara.
Da yake gabatar da rahoton hukumar cikin harshen turanci Zikrullah, ya bayyana nasarori da kuma kalubalen da NAHCON ta fuskanta a aikin Hajjin da ya gabata na 2023.
Da yake karin haske akan ziyarar cikin harshen Hausa Kwamishina mai kula da harkokin kudi da ma’ailata da tsare-tsare na hukumar NAHCON Alhaji Nura Hassan Yakasai yace baya ga kalubalen da suka fiskanta sun kuma samu nasarori kamar kwashe daukacin Alhazan Najeriya suka biya kudi akan lokaci tare da basu damar kai ziyara Madina kafin zuma Makka da da sauransu.
Haka kuma ya tabbatar da yin iya bakin kokarinsu wajen cigaba da gudanar da aikinsu da shawarwarin da maitaimakin shugaban kasar ya basu.
Akarshe ya godewa mataimakin shugaban Kasar bisa goyon bayan da hadin kan da yake basu wajen gudanar da aikinsu .
Tawagar ta Kunshi daukacin kwamishinoni da sauran ma’aikatan Hukumar kula da aikin Hajjin ta Kasa NAHCON.