A kokarin da take yi na rage cinkoso a gidajen gyaran hali, gwamnatin tarayya ta biya tara da kuma diyya na Nairamilliyan 52 ga fursunoni 399 a cibiyoyi daban-daban a fadin jihar Kaduna.
Kwanturolan hukumar kula da gidan gyaran hali na jihar Kaduna, Dr Ado Saleh ne ya bayyana hakan a yayin kaddamar da shirin a Zaria a ranar Litinin, inda ya ce an sako fursunonin 68 daga cibiyoyi na gyaran hali na Zaria da Makarfi da Soba da kuma Ikara.
Ya ce tun da farko an saki fursunoni 110 a Kaduna, inda ya ce bikin da aka yi a Zaria ci gaba ne na shirin da gwamnatin tarayya ta tsara tare da aiwatarwa.
Kwanturolan ya kara da cewa za’a baiwa kowane daya daga cikin wadanda suka amfana da shirin Naira dubu 10 a matsayin kudin Mota domin komawa gida.