On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Gwamnatin Najeriya Ta Biya Billiyan 169.4 Amatsayin Tallafin Man Fetur A Watan Agusta 2023

Alamu sun nuna cewa gwamnatin tarayya ta biya Naira biliyan 169.4 amatsayin tallafi a watan Agusta domin cigaba da samun farashin man Fetur akan Naira 620 kowace lita.

Wannan na zuwa ne duk da irin tabbacin da shugaba Bola Tinubu ya sha bayarwa cewa tallafin mai ya tafi kenan.

Wani kundi na kwamitin kasafta arzikin kasa wanda jaridar dailytrust ta gani, ya nuna cewa a cikin watan Agustan 2023, Kamfanin gasa na kasa  NLNG ya biya dala milliyan 275 amatsayin ribar kamfanin NNPC Limited.

Bayan haka, kamfanin NNPC Limited ya yi amfani da dala miliyan 220 kwatankwacin Naira billiyan 169.4 daga cikin dala miliyan 275 wajen biyan tallafin man fetur, inda aka yi zargin cewa ya rike dala miliyan 55 ba bisa ka'ida ba.

Wannan dai ya karfafa  ikirari da shugaban PENGASSAN na kasa, Festus Osifo ya yi cewa saboda tsadar danyen mai a kasuwannin duniya da kuma karuwar farashin canji, har yanzu gwamnati na biyan tallafin man fetur.