Ma’ikatar harkokin wajen Najeriya ta bayyana dalilan dake haifar da jan kafa wajen dawo da ‘yan Najeriya 300 da suka makale a hadaddiyar daular larabawa.
Ma’aikatar tace tana aiki tare da offishin jakadancin Najeriya dake Daulara larabawa da offishin jakadancin kasar dake Najeriya da sauran hukumomi kan yadda za’a dawo da ‘yan najeriya da suka makale saboda dalilai daban-daban, da suka hadar da batan Paspo da rashin takardu musamman ga jarirai wanda al’amarin ke hannun rundunar ‘yan sandan kasar..
Bayanin hakan na kunshe a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ma’aikatar Francisca Omayuli ta fitar.
Sanarwar tace ‘yan najeriya da al’amarin ya shafa suna cikin ‘yan Afirka da suke tsare a offishin kula da shige da fice na kasar har sai an gama bin matakan shari’a da doka daga hukumomi kafin a dawo da su gida.