On Air Now

ZANGON RANAR ASABAR

Noon - 6:00pm

Gwamnatin Najeriya Ta Ayyana Ranakun Hutun Kirsimeti Da Sabuwar Shekara

Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Litinin 26 da Talata 27 ga watan Disamba a matsayin ranakun hutun  Kirsimati.

Ministan cikin gida Ogbeni Rauf Aregbesola shine ya sanar da hutun a madadin gwamnatin tarayya ta cikin wata sanarwa dauke da sahannunsa da ma’aikatarsa ta fitar ranar Alhamis.

Sanarwar ta ce ranar Litinin 2 ga watan Junairun 2023 zata zama ranar hutun sabuwar shekara.

Aregbesola ya yi amfani da wannan dama wajen taya mabiya addinin Kirista a daukacin Najeriya murnar bikin Kirsimati da suke gudanarwa duka shekara, domin tunawa da ranar haihuwar Annabi Isa Alaihis-salam.

Ya bukaci su yi koyi da kyawawan halayaensa da littafin Bibble ya sanar da suka hada da hakuri da kyautatawa da koyarwa da taimako da sauransu.

Ogbeni Rauf Aregbesola ya tunatar da daukacin 'yan Najeriya da ke shirin bikin sabuwar shekara, cewa shekarar 2023 ne za a yi babban zabe, saboda haka su zama cikin shirin kada kuri'a da zaben shugaban da ya cancanci magance  matsin tattalin arziki da inganta da tsaro da ilimi da kuma kiwon lafiya.