Gwamnatin tarayya ta ayyana ranakun Juma’a da Litinin 21 da kuma 24 ga watan Afrilu a matsayin ranakun hutu domin gudanar da bukukuwan karamar Sallah a bana.
Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, shine ya bayyana hakan a wata sanarwa da babban sakataren na ma’aikatar sa, Dr Shuaib Belgore, ya fitar ranar Laraba.
Ya kuma taya daukacin al’ummar musulmi murnar kammala azumin watan Ramadan lafiya.
Aregbesola ya yi kira ga daukacin al’ummar Musulmi da su yi koyi da kyawawan dabi’u da soyayya da hakuri da zaman lafiya da sadaukarwa irin na Annabi Muhammadu S.A.W.