Gwamnatin Najeriya ta gargadin malaman jami’oin kasarnan akan kin yin biyayya ga Kotun ma’aikata da ta bada umarni malaman su janye yajin aikin da suke gudanarwa.
Ministan kwadago Chris Ngige ya yi wannan gargadi ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ma’aikatar kwadago Olajide Oshundun ya fitar a Abuja.
Sanarwar ta ruwaito Ngige na ikirarin cewa ASUU bata da gaskiya kuma tana yaudarar jama’a cewa ta shigar da kara da kuma dakatar da aiwatar da hukuncin kotu, duk da cewa ba ta da komai kuma bata yi komai a kasa ba.
Ya ce ASUU ta shigar da bukatar neman izinin daukaka kara ne kawai kuma ba a ayyana lokacin sauraren karar ba.
Sai dai ministan ya bayyana kin bin umarnin kotu da ASUU a matsayin rashin bin doka da oda.