Majalisar zartaswa ta tarayya ta amince da neman lamuni na dala biliyan 3.45 domin gudanar da ayyuka biyar a bangaren samar da wutar lantarki da sabuwar fasahar makamashi.
Da yake magana a karshen taron da ya gudanar a ranar Litinin, ministan kudi kuma mai kula da harkokin tattalin arzikin kasa, Wale Edun, ya ce ayyukan da aka amince da su sun kasance a cikin wasiku biyar da ya gabatar.
Edun ya ce takardun da shugaban kasa Bola Tinubu wanda ya jagoranci taron ya amince da su sun hada da lamuni ba tare da kudin ruwa ba daga bankin duniya da kuma kungiyar ci gaban kasa da kasa.
Haka kuma an amince da bayar da kudade don shirye-shiryen tattara albarkatun kasa a jihohi don taimaka musu da kokarin samun kudaden shiga.