On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Gwamnatin Najeriya Na Barazanar Daina Biyan Albashi Ga Ma'aikatan Da Suka Bijirewa Rijista Da IPPIS

Gwamnatin tarayya ta yi barazanar daina biyan albashin  duk wani Ma’aikacin gwamnati da  bayanansa  basa cikin tsarin tantace bayanan biyan albashi na  Bai daya IPPIS daga ranar  juma’a mai zuwa  27 ga watan da muke ciki.

Shugabar ma’aikata ta Kasa, Dr Folasade Yemi-Esan ce ta bayyana hakan  ta  cikin wata sanarwa da Daraktan yada labaranta Mohammed Ahmed ya fitar.

A cewar sanarwar, An fara aikin tantancewar  ne ta  tsawon mako biyu, wadda za ta  kare a ranar Juma’a, domin  inganta hanyoyin biyan albashi ga  ma’aikata.

Ta yi gargadin cewa ba za a kara biyan duk wani albashi  ga ma’aikacin gwamnati da  bayanansa  basa cikin tsarin.