Yanzu haka jama’a na cigaba da yama’di-‘di da matakin da gwamnatin jihar Legas ta dauka na amincewa da kashe zunzurutun kudi har naira naira milyan 61 da dubu 200, domin yin gagarumin bukin binne mutane 103, wadanda suka gamu da ajalinsu a shekarar 2020, sakamakon zanga-zangar ENDSARS, data barke a jihar.
Idan ba’a manta ba, Gwamnatin jihar da kuma rundunar soji ta kasa sun ga baiken rahoton da kwamitin bincike ya fitar, wanda ya nuna cewar anyi kisan kiyashi a yankin Lekki Toll Gate, a lokacin da sojoji suka bude wuta, a ranar 20 ga watan Octoban 2020.
Sai dai wata wasika da mai dauke da kwananan wata,19 ga watan da muke ciki,da hukumar kula da bada kwangilolin gwamnati ta jihar Legas ta fitar, Ta nuna cewar,gwamnatin jihar ta dauki hayar wani kamfani mai suna Tos Funeral Ltd, domin yin aikin binne mamatan guda 103 akan kudi naira milyan 61 da dubu 200.
Wasikar dai ta haifar da cece kuce a tsakanin mutane, musamman masu ‘yan gwagwarma ya, wanda ke nuna rashin amincewarsu da daukar matakin, duk da cewar a baya gwamnati da hukumomi sun musanta cewar anyi kisan kiyashi a wajen.
A wani bangaren kuma, Gwamnatin jihar Legas ta mayar da martani kan cece-kucen da jama’a ke yi dangane da fitar da makudan kudin domin binne gawarwakin mutanen.
Wata sanarwa da babban sakatare a ma’aikatar Lafiya ta jihar Legas, Dr Olusegun Ogboye ya fitar a daren jiya, Ta yi ikirarin cewar daga cikin mutanen 103 da suka mutu, babu wanda aka samu a yankin Lekki Toll Gate.
Bugu da kari yace gwamnatin jihar ta amince da shirya yin gagarumin bukin binne mutanen ne a lokaci daya, bayan kwashe shekara ukku ana gaiyatar yan uwa da masoyan wadanda ba’a gani ba a lokacin zanga-zangar, amma kuma babu wanda ya je domin duba dan uwansa ko wani nasa da ba’a gani ba saboda zanga-zangar.