On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Gwamnatin Kano Zata Kafa Kwamitin Nemarwa Daliban Kano Guraben Karatu

KOFAR MATA

Gwamnatin jihar Kano na wani yunkuri na kafa kwamitin nemowa ‘yan jihar Kano Guraben karatu, domin tabbatar da cewar ‘yan asalin jihar kano, sun rika cin gajiyar guraben karatun da ake ware masu a manyan makarantun kasar nan.

Kwamishinan Ilimi  na mai zurfi na  jihar Kano,Dr.Yusuf Ibrahim Kofar mata ne ya baiyana haka a yayin wani taron masu ruwa da tsaki  da aka shirya a kwalejin share fagen shiga  jami’a dake nan Kano.

Sanarwar da kakakin ma’aikatar  Sunusi A kofar Naisa ya  fitar, ta Ambato  kwamishinan na cewar matakin zai rage yawan dogara da manyan makarantun da ake dasu a jihar Kano, wajen samun  guraben karatu.