On Air Now

ZANGON RANAR ASABAR

Noon - 6:00pm

Gwamnatin Kano Zata Kaddamar Da Rabon Tallafin Rage Radadi Bayan Cire Tallafin Man Fetur A Najeriya

A yau ne gwamnatin jihar Kano za ta kaddamar da rabon kayan abinci a matsayin wani bangare na rage radadi, watanni uku bayan cire tallafin man Fetur da shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yi.

Al’ummar Kano dai sun dade suna dakon matakan da za’a dauka na samar da saukin tsadar rayuwa, kuma a kwanakin baya wasu mata ma sun gudanar da zanga-zangar lumana suna neman a saukaka farashin abinci bayan da gwamnatin tarayya ta amince da Naira billiyan 5  ga kowace jiha.

Sai dai a iya cewa jira ya kare a yanzu inda mai magana da yawun gwamna Abba Yusuf, Sanusi Bature ya tabbatar da safiyar yau a cikin wani gajeren sako da ya aike wa manema labarai cewa za a fara raba kayan abinci a yau.

Ya ce taron zai gudana ne a hukumar bunkasa aikin gonad a raya karkara ta Kano KNARDA da karfe 11 na safe ba tare da wani karin bayani ba.