On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Gwamnatin Kano Ta Sauke Shugaban Asibitin Hasiya Bayero

Hukumar kula da asibitoci ta jihar Kano ta sauke shugaban asibitin yara na Hasiya Bayero bisa zargin rashin iya shugabanci.

Wata sanarwa dauke da sahannun jami’ar hulda da jama’a ta hukumar Samira Suleiman, ta ce an dauki matakin ne bayan doguwar tattaunawa da kwamishinan lafiya Dr. Abubakar Yusuf Labaran da shugaban hukumar kula da asibitoci ta jihar Kano, Dr. Mansur Mudi Nagoda.

Sanarwar ta zargi shugaban asibitin na Hasiya Bayero da aka sauke da gazawa wajen tsara ma’aikata tare da aiwatar da manufofin gwamnati da aka ayyana na duba marasa lafiya  da kuma kula da su kyauta.

Sanarwar ta kuma ruwaito Dr. Nagoda na korafin cewa shugaban ya gaza sarrafa ma’aikatansa domin samar da kulawa yadda ya kamata.

An sanar da Dr. Ibrahim Ibn Muhammad amatsayin sabon shugaban  asibitin na Hasiya Bayero.