Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Abba Kabir Yusuf, Ta rushe shatale-talen kofar shiga gidan gwamnatin kano, da tsohuwar gwamnatin Ganduje ta gina.
A daren jiya ne aka yi aikin rushe wajen, har zuwa wannan lokaci dai, gwamnati jihar kano bata fitar da wata sanarwa a kan dalilin da ya sa ta rushe shatale-talen da aka kaddamar a lokacin da tsohuwar gwamnati ta yi bukin cikar kano shekara 50 da kafuwa.
Sai dai idan ba’a manta ba, Gwamnatin Kano na cigaba da rushe haramtattun gine-gine da aka yi su a filayen gwamnati, a wani bangare na cika alkawarin da ta dauka a lokacin yakin neman zabe.