Shugaban Hukumar Kula da Asibitoci ta Jihar Kano, Dakta Mansur Mudi Nagoda, ya musanta rahoton da aka wallafa a kafafen sada zumunta cewa marasa lafiya 10 sun mutu a rana daya a asibitin koyarwa na Muhammad Abdullahi Wase.
An ruwaito wani Husaini Ahmad ya yi zargin cewa majinyata 10 ne suka mutu a wannan rana a asibitin, inda ya danganta mutuwar da sakacin jami’an asibitin.
Sai dai wata sanarwar hadin gwiwa da hukumar da ma'aikatar lafiya ta jihar Kano suka fitar, ta ce an gudanar da bincike ba tare da bata lokaci akan bayanan asibitin daga ranar 1 ga watan Oktoba zuwa 10 ga watan Oktoba kuma ba a gano matsalar da ake zargi bat a mutuwar mutane 10 a rana guda.
Sanarwar ta kara da cewa, asibitin ya gudanar da bita ta kwanaki 10 kan mace-macen a duk fadin asibitin, inda aka gano cewa majinyata 15 ne kawai suka mutu a cikin kwanakin kuma a ranaku daban-daban.