Gwamnatin jihar Kano ta kafa wani kwamitin kwararru da zai binciki yadda aka fuskanci ambaliyar ruwa sakamakon mamakon ruwan sama cikin ‘yan kwanakin nan.
Kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Muhammad Garba, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, yace gwamnati ta damu matuka game da afkuwar ambaliyar ruwa da ta yi sanadin asarar rayuka da dukiyoyi.
Garba ya ce an dora wa kwamitin nauyi da alhakin yin nazari kan manyan hanyoyin mota da magudanan ruwa dake cikin mummunan yanayi, da nufin gyara su da kuma sake gina wasu idan akwai bukatar hakan.
Ya yi kira ga jama’a da su yi hakuri kasancewar gwamnati za a yi duk mai yiwuwa wajen ganin an magance matsalar.