Gwamnatin jihar Kano ta kafa kwamitin mutum 22 domin tantance ma’aikata kusan dubu 10 da 800 da aka dauka aiki a karshen wa’adin gwamnatin da ta gabata ta Dr. Abdullahi Umar Ganduje.
Sakataren gwamnatin jihar Kano, Dr. Baffa Bichi, ya ce kwamitin zai tabbatar da ko anbi ka’ida wajen daukar ma’aikata sama da dubu 10.
Kwamitin zai yi aiki bisa jagorancin shugaban hukumar daukar ma’aikata, Alhaji Umar Shehu Minjibir, kuma an baiwa kwamitin wa’adin makonni uku ya kammala aikinsa.
A martanin da ya mayar, Minjibir ya yi alkawarin cewa mambobin kwamitin za su yi iya kokarinsu don ganin sun kammala aikin a kan lokaci.