On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Gwamnatin Kano Ta Kaddamar Da Kwamitin Mutum 11 Domin Yaki Da Sha Da Fataucin Miyagun Kwayoyi

Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da wani kwamiti na mutum 11 da aka dora wa alhakin magance safara da ta'ammali da muggan kwayoyi a jihar

Shugabar kwamatin, Kuma Mai bada shawara ta musamman ga gwamnan jihar Kano kan harkokin kiwon lafiya, Dakta Fauziyya Buba Idris, tace hakan  wani bangare ne na gudanar da bikin ranar yaki da  sha da fataucin miyagun kwayoyi ta duniya a bana, wadda ake gudanarwa a ranar 26 ga watan Yuni na kowace shekara.

Dokta Buba ta ci gaba da cewa, shaye-shayen miyagun kwayoyi ya kasance babban abin da ke haifar da yawaitar miyagun ayyuka a kasar nan.

Wakilin Bashir Faruk Durumin Iya, ya ruwaito Dokta Buba na cewa kwamitinsu zai yi aiki a daukacin kananan hukumomin 44 domin wayar da kan al’umma kan illolin shan miyagun kwayoyi.