On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Gwamnatin Kano Ta Fara Aikin Feshin Maganin Sauro Da Kwari A Makarantun Kwana Da Tsangaya

Gwamnatin jihar Kano ta yi alkawarin gudanar da Feshin magungunan kwari da sauro a makarantun kwana da Tsangaya a wani mataki na yaki da kananan cututtuka tsakanin al'umma.

Kwamishinan muhalli na jihar Kano Alhaji Nasiru Sule Garo ne ya yi wannan alkawari lokacin da yake kaddamar da shirin Feshin magungunan kwari   domin yaki da kananan cututtuka musamman cutar zazzabin cizon sauro da yake damun al’umma a wani taron da aka gudanar a sakandiren Fasaha ta  GTC Ungogo dake Kano.


Nasiru Sule Garo ya ce, bayan kaddamar da aikin, gwamnatin jihar Kano za ta tabbatar anyi feshin a dukkanin makarantun kwana da makarantun tsangaya.

Ya ce  feshin maganin zai kawai da  sauro da  Beraye, Micizai da sauran Kwari da zasu iya cutar da al’umma, kuma feshin ya kamata ace ana yin sa duk shekara, inda ya bada tabbacin cewa gwamnatin ta injiniya Abba Kabir Yusuf, za ta Alaiwatar da duk wani aiki   da amince domin cigaban mutanen Kano.

Kwamishinan ya ce matukar gwamnatin Injiniya Abba Kabir Yusuf ta cigaba da rike madafun iko, gwamnatin za ta tabbatar anyi feshin maganin a kowacce shekara a don inganta lafiyar alumma.

Ya kuma bukaci hadin kan masu ruwa da tsaki da su tabbatar da aikin feshin ya yi nasara.


A na sa jawabin, kwamishinan ilimi na jihar Kano Umar Haruna Doguwa wanda shugaban makarantun sakandiren kimiya da fasaha na jihar Kano ya wakilta ya yabawa gwamnatin Kano bisa farfado da shirin a makarantun sikandiren wanda darakta a hukumar Alhaji Garba Ahmed ya wakilta ya bada tabbatar ma'aikatar ilimi da hukumar na ganin shirin ya samu nasara domin kula da lafiyar dalibai.

Shi kuwa, shugaban makarantar sakandiren  GTC Ungogo Malam Mikail Hussain ya ce feshin ya.zo a  dai-dai al lokacin da ake bukatar  laakari da yadda daliban makarantar ke  fama da  cutar zazzabin cizon sauro a baya-bayan nan.