Gwamnatin jahar Kano ta haramta yin amfani da wasu littafan karatu a daukacin makarantun Nursery da Firamare da kuma Sakandire a fadin jahar kano saboda illolin dake tattare da littafan da kuma yadda suke koyar Alfasha a cikinsu.
Bayanin hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke dasa hannun daraktan bincike da kididdiga na ofishin mai bawa gwamnan kano shawara kan harkokin makarantu masu zaman kansu da kuma sa kai, Hamisu Ibrahim.
Sanarwar ta baiyana sunayen littafan da matakin ya shafa wanda suka hada da wani littafi mai Suna Queen Premier da wasu littafan koyar da kimiyya ga kananan makarantun sakandire mai suna Basic Science wallafawar RAZAT bugun shekarar 2018 da kuma wani littafin koyar da kimiyya mai suna Acticve Basic Science bugun shekarar 2014, wallafawar Tola Anjorin da Okochuku okolo sai Philias Yara da Bamidele Mutiu da kuma Farima Kaki.
Sauran littafan sun hada dana koyar da kimiyya da fasahar kere-kere na kananan makarantun sakandire mai suna Basic Scince anda Techonology wallafar W.K Hamzat Da S Bakare sai kuma wani littafin koyar da harshen turanci mai suna New Concept Englis bugun shekarar 2018 da kuma wani littafin koyar da ilimin zamantakewa mai suna Basic Social Studies na ‘yan makarantun Firamare wallafar J Obebe.
A wani bangaren kuma, Hukumar tace fina-finai da ‘Dab’I ta jahar kano ta ce ta kwace dukkanin wasu littafai masu suna Queen Premier biyo bayan koken da jama’ar gari suka yi akan illolin dake kunshe a cikin littafin wanda suka saba da koyarwar addinin musulunci.
Hukumar karkashin shugabancin Alhaji Abba El Mustapha ta ce ta yi amfani da ikon da doka ta bata wajen daukar wannan mataki.
Wata sanarwa da jami’in yada labaran hukumar Abdullahi Sani Sulaiman ya fitar a ranar Alhamis, ta Ambato shugaban hukumar na cewar, Hukumar ta hana yin duk wani film ko littafi ko kuma wata wallafa wadanda suke kunshe da bayanan batsa a cikinsu, saboda ya saba da tarbiya da kuma koyarwar addinin musulunci