On Air Now

ZANGON RANAR ASABAR

Noon - 6:00pm

Gwamnatin Kano Ta Dakatar Da Wasu Shugabannin Makarantun Sakandire

Gwamnatin jihar Kano ta bayar da umarnin dakatar da wasu shugabannin makarantun sakandire guda uku ba tare da bata lokaci ba saboda laifin fashin zuwa  wurin  aiki.

Makarantun da abin ya shafa sun hada da G.G.S.S. Dawanau, da G.G.S.S. ‘Kwa da  kuma G.A.S.S. Dawanau duk a karamar hukumar Dawakin Tofa.

Kwamishinan ilimi na jihar Kano Hon Umar Haruna Doguwa ya bayyana haka ne jim kadan bayan ya ziyarci makarantun da karfe 9 zuwa 10 na safiyar yau Juma’a, inda ya gano cewa shugabannin da abin ya shafa ba su je wuraren aikinsu ba.

Daga binciken da ya gudanar, dukkan jami’an uku sun saba kauracewa zuwa aiki a ranakun Juma’a, tsahon wani dan lokaci.

Kwamishinan ya kuma ba da umarnin a tura sabbi kuma kwararrun shugabanni a makarantun uku, domin tabbatar da cewa ba a samu cikas na harkokin koyo da koyarwa ba.

Hon Umar Doguwa ya kuma ba da umarnin rubuta wasikar neman bahasi ga wasu malamai hudu a GGSS Kwa da biyu a GASS Dawanau.

Haka kuma kwamishinan ya ba da umarnin yabawa ga shugabar makarantar G.G.S.S. Harbau dake  karamar hukumar Tsanyawa, saboda jajircewarta.