On Air Now

ZANGON RANAR ASABAR

Noon - 6:00pm

Gwamnatin Kano Ta Ayyana Hutun Sabuwar Shekarar Musulunci

Gwamnatin jihar Kano ta ayyana gobe Laraba, 19 ga watan Yuli, 2023 a matsayin ranar  hutu domin murnar shiga sabuwar shekarar musulunci  ta 1445.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kwamishinan yada labarai Baba Halilu Dantiye a madadin gwamna Abba Kabir Yusuf. 

Gwamnan wanda ya taya al’ummar musulmin duniya murnar zagayowar sabuwar shekara ta Musulunci, ya kuma bukaci ma’aikatan gwamnati da sauran al’ummar jihar Kano da su yi addu’ar Allah ya kawo  zaman lafiya da kwanciyar hankali tare da bunkasa tattalin arzikin jihar da kasa baki daya. 

Gwamnan ya kuma yi kira ga al’umma da su rika gudanar da rayuwarsu bisa koyarwar addinin Musulunci tare da kyawawan dabi’u na kyautatawa da soyayya da kuma hakuri da juna kamar yadda Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallama (S.A.W) ya koyar.