Hukumar korafe-korafen jama'a da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano tace ta fara bincike kan zargin karkatar da wasu kudade sama da naira biliyan 100 na kananan hukumomi da tsohuwar gwamnatin Dr. Abdullahi Umar Ganduje ta yi.
Hukumar ta ce ta bi diddigin yadda aka karkatar da wasu kudaden har zuwa karshe, cikin shekaru hudu.
Shugaban Hukumar, Barista Muhuyi Magaji Rimingado ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a lokacin da ya karbi bakuncin mambobin kungiyar hadin gwiwa ta jihar Kano kan tafiyar da gwamnati a bude.
Ya koka da yadda yaki da cin hanci da rashawa ke da kalubale da yadda matsalar tayi nisa a cikin al’umma.