Hukumar kula da ilimin bai daya ta jihar Kaduna ta kori malamai dubu 2 da 357 saboda rashin samun nasarar cin jarabawar cancanta da aka gudanar a jihar.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, Jami’ar hulda da jama’a ta hukumar Hauwa Mohammed, ta ce malaman firamare dubu 2 da 192 ciki harda shugaban kungiyar malamai ta kasa NUT saboda sun ki rubuta jarabawar.
A cewarta, an kuma kori wasu malamai 165 daga cikin dubu 27 da 662 da suka rubuta jarrabawar cancantar saboda rashin nuna kwazo.
Da yake mayar da martani, shugaban kungiyar NUT na jihar, Ibrahim Dalhatu, ya bayyana jarabawar cancantar da sallamar malaman a matsayin haramtaccen mataki domin kungiyar ta samo umarnin kotu na hana hukumar gudanar da jarabawar.
Ya ce kungiyar ba ta adawa da gudanar da jarabawar, amma bai kamata a yi amfani da ita wajen korar malamai ba.