On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Gwamnatin Jihar Zamfara Ta Bada Damar Mallakar Bindiga Ga Al’umma Domin Kare Kansu

Gwamnatin jihar Zamfara ta bai wa dukkan 'yan Jihar damar mallakar bindiga domin kare kansu daga 'yan fashin daji da masu garkuwa da mutane.

A wata sanarwa da Kwamishinan watsa labaran Jihar, Ibrahim Magaji Dosara, ya aike wa manema labarai ranar Asabar, ya ce gwamnati ta dauki matakin ne sakamakon yawaitar hare-haren 'yan ta'adda da 'yan fashin daji.

 

Gwamnatin Zamfara ta dauki matakin ne watanni da dama bayan gwamnatin Jihar Katsina da ke makwabtaka ta umarci mazauna jhar su mallaki bindiga domin kare kansu daga masu kai hare-hare.

 

Sanar tace hare-haren ta'addanci sun kasance ababen  damuwa ga jama'a da gwamnati saboda haka domin  magance wannan matsala baki daya, gwamnati ba ta da zabin da ya wuce daukar matakan da suka hada da bai wa mutane damar shiryawa da kuma mallakar bindigogi domin kare kansu daga 'yan fashin daji.

 

Ta kara da cewa gwamnati ta umarci Kwamishinan 'yan sanda ya bai wa dukkan mutanen da suka dace da kuma suke bukatar mallakar bindiga su mallake ta domin kare kansu.

 

Gwamnatin ta Jihar Zamfara ta ce ita da kanta za ta shige gaba wajen ganin an saukakawa mutane hanyar mallakar bindiga, musamman ga "manoma domin samun makaman da za su kare kansu."

 

Tuni gwamnati ta kammala shirin raba fom 500 ga masarautu 19 da ke Jihar nan domin bai wa mutanen da ke bukatar mallakar bindigogi domin su kare kansu.