Gwamnatin Filato ta ce za ta hada gwiwa da wani kamfani mai zaman kansa, United Capital, domin biyan kusan Naira biliyan 18 na gratuti da hakokin Magada da kuma sauran bashin da ma’aikatanta ke bi baya.
Kwamishinan yada labarai da sadarwa na jihar Mista Dan Manja, shine ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a karshen taron majalisar zartarwa ta jiha a ranar Laraba a Jos.
Manja ya ce majalisar ta amince da sake bibiyar farashin kadarori da ke karamar hukumar Shendam ga ma’aikatanta da suka yi ritaya, biyo bayan roko da suka yi kan wahalar biyan kudin gidajen da filin da aka ware masu shekaru da dama da suka gabata. .
Ya ce an sanar da majalisar cewa Gwamna Simon Lalong ya amince tare da fitar da kudi Naira miliyan 114 a matsayin kudin lasisin fara aiki ga gidan rediyo da talbijin na Filato, inda ya ce a halin yanzu kamfanin ya na da tsarin zamani wajen biyan kudaden.