Sama da gine-gine 100 ne hukumar kula da gine-gine ta jihar Legas ta rushe a cikin watanni 8 da suka gabata, a wani mataki na dakile rugujewar gine-gine a jihar.
Alkaluman da aka tattara daga shafin yanar gizo na hukumar kula da gine-ginen ta Legas sun nuna cewa gine-ginen da aka rushe ruguje a cikin tsukun lokacin sun hada da wadanda suka tsufa da gine-ginen da ba su da Inganci da wasu haramtattun gine-gine da kuma gidaje.
Sakamakon binciken ya nuna cewa, a cikin watanni biyun da suka gabata gwamnatin jihar ta rusa akalla gine-gine 23 da ake ganin ba za a iya cigaba da wanzuwa ba ko kuma za su iya haifar da hadari ga rayuka da dukiyoyin al’umma.
Da ya ke mayar da martani game da rushe-rushen da gwamnatin jihar Legas ta yi a baya-bayan nan, Wani kwararre kan gine-gine, Chukwurah Godfrey, ya ce matakin ya zama dole domin ceton rayuka da dukiyoyi.