Gwamnatin jihar Katsina ta haramta siyarwa da kuma shan Shisha da sauran dukkanin wasu abubuwan saka Maye a fadin jihar batare da bata wani lokaci ba.
Bayanin haramcin na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai na gwamnatin jihar Buhari Mamman Daura ya fitar jiya juma’a a jihar Katsinan Dikko.
Yace haramta siyarwa da kuma shan Shisha da sauran abubuwa masu bugarwa na daga cikin dokokin da gwamnan jihar Aminu Masari ya sanyawa hannu a ranar 5 ga watan da muke ciki.
Gwamna Aminu Masari
Yace gwamnati ta dauki matakin ne la’akari da karuwar matasan da ta’amulli da Shisha a jihar, kuma yace duk wanda aka samu da karya dokar za’a hukunta shi bisa tanadin sashi na 114 da kundin dokokin Penal Code na jihar Katsina na shekarar 2021.