On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Gwamnatin Jihar Kano Ta Rubanya Kudaden Tafiyar Da Masautu Biyar Na Jihar

Majalisar zartaswa ta jihar Kano ta amince da karin kashi 100 na kudaden tafiyar da masarautun jihar guda 5 da take basu duk wata.

Kwamishinan yada labarai Comrade Mohammad Garba ne ya sanar da hakan ranar alhamis yayin taron  manema labarai kan sakamakon zaman majalisar zartaswa da aka gudanar ranar laraba.

Kwamishinan ya kuma kara da cewa biyo bayan wannan cigaba, an kara yawan alawus-alawus na majalisar masarautar Kano na wata wata zuwa miliyan 100 daga naira miliyan 50, yayin da kuma saura zasu rika karbar naira miliyan 40.

Yayi bayanin cewa karin zai taimaka wajen rage radadin tabarbarewar tattalin arziki da ake fuskanta a Najeriya.

Wakilin Arewa Radiyo Abdulrahaman Balarabe Isah, ya rawaito  kwamishinan yada labaran na jihar Kano Mohammad Garba ya tabbatar da cewa majalisar zartaswar jihar Kano ta amince da sakin sama da naira miliyan dari 3 domin biyan alawus alawus da malaman jami’ar Yusuf Maitama Sule ke bin gwamnati.

Kwamishinan ya bayyana cewa za’a yi amfani da sama da naira miliyan dari 2 wajen biyan alawus alawus da malaman jami’ar ke bi, yayin da kuma za’a yi amfani da miliyan 6 wajen biyan ma’aikatan jami’ar da ba’a biya su alawus dinsu na karshe da aka biya ba.

Ya kuma kara da cewa naira miliyan 8 kuma za’a yi amfani da ita wajen yiwa jami’ar kwaskwarima tare kuma da samar da kayayyaki a sashen kimiyya da fasaha na jami’ar.