Gwamnatin jihar Kano ta rabawa asibitocin jihar Kano da kayayyakin kiwon lafiya kyuata na kimanin Naira miliyan goma sha biyar.
Babban Daraktan Hukumar Kula da Asibitoci ta jihar Kano Dr Nasiru Alhasan Kabo shine ya bayyana haka a lokacin da ya kaddamar da rabon kayayyakin ga asibitocin a nan Kano.
Kabo wanda Daraktan kula da sashin Likitanci na hukuamr, Dr Sulaiman Mudi Hamza ya wakilta ya ce za a yi amfani da kayayyakin ne a wuraren kula da mata masu juna biyu, da sashin bada agajin gaggawa na asibitoci da kuma kula da lafiyar kananan yara.
Wakilinmu Bashir Faruk Durumin Iya ya ruwaito mana cewa wata kungiya mai zaman kanta dake karkashin Asusun amintattu na kula da bangaren Lafiya ta ba da gudummawar Naira Milyan 5m domin aiwatar da shirin.