On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Gwamnatin Jihar Kano Ta Kudiri Aniyar Kammala Titin Wuju-Wuju Cikin Kwana 'Dari Na Farko

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya bada tabbacin cewa gwamnatinsa zata kammala aikin titin Wuju-Wuju mai tsawon kilomita 1.2 kafin cika kwanaki dari na farkon gwamnatin sa.

Gwamnan ya bada tabbacin ne a lokacin da ya kai ziyarar duba yadda ake gudanar da aikin yayin da ‘yan kwangila suka koma bakin aikin.

Gwamna Abba ya bayyana farin cikinsa da cewa an bayar da kwangilar ne a zango na biyu na gwamnatin Kwankwaso.

Ya ce aikin da aka tsara don magance matsalar sauyin yanayi a Kano, gwamnatin da ta shude ta yi watsi da shi a shekarar 2015.