Gwamnatin jihar Kano ta yabawa kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars bisa nasarar da ta samu a wasan daf da na kusa da karshe a gasar cin kofin Aiteo da ke cigaba da gudana.
Mukaddashin gwamnan jihar, Nasiru Yusuf-Gawuna shine ya yi wannan yabo a cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaran sa, Hassan Musa-Fagge, ya fitar a karshen mako.
Ya ce nasarar da Pillars ta samu daci 2-0 akan kungiyar DMD ta Maiduguri a zagaye na kungiyoyi 16 na gasar cin kofin Aiteo da aka gudanar a Bauchi a ranar Asabar abin yabawa ne.