On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Gwamnatin Jihar Kano Ta Hana Makarantar Kano Capital Karin Kudin Makaranta Ga Dalibanta

Gwamna Ganduje

Ma’aikatar Ilimi ta jihar Kano ta umarci hukumar gudanarwa ta makarantar Kano Capital data janye sabon karin kudin makaranta data yi.

Babbar sakatariya a ma’aikatar Hajiya Lauratu Ado Diso ce ta bayar da wannan umarni yayin da take kaddamar da kwamitin da zai yi nazari kan rahotannin makarantar na  baya da aka gabatarwa  ma’aikatar domin aiwatarwa.

Babbar sakatariyar ta tabbatarwa iyayen Daliban da abun ya shafa cewar ma’aikatar zata tabbatar komin an dorashi kan gurbinsa, ta hanyar amfani da ka’idoji da kuma doka, inda ta bukace su dasu kwantar da hankalinsu  sannan kuma su kasance masu bin doka.

Ta kara da cewa  an kafa kwamitin ne domin yin nazari kan rahotanni baya na makarantar da aka gabatar masu game da wasu matsaloli da aka gano a makarantar  domin  aiwatarwa.