Gwamnatin jihar Kano ta shigar da bukatar janye karar da aka shigar gaban babbar kotun tarayya da ke Kano kan hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC, dake neman hana ta binciken tsohon gwamna Abdullahi Ganduje kan badakalar cin hanci dake cikin faifan bidiyon Dala.
Kwamishinan shari’a kuma babban lauyan jihar Kano, Barista Haruna Dederi ne ya fara daukar matakin.
Takardar ta sanar da kotun cewa gwamnati bata da aniyar hana EFCC ci gaba da gayyata ko bincike ko kuma yi wa tsohon shugaban hukumar SUBEB da darakta kudi na hukumar da kuma Akanta Janar na jihar Kano tambayoyi dangane da faifan bidiyo na zargin karbar cin hanci.
A cikin sanarwar neman Janye karar da Jami’a a Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kano, AminaYargaya, ta gabatar, an gabatar da bukatar ne a bisa doka ta 50 ta Babbar Kotun Tarayya ta 2019 da aka yiwa gyaran Fuska.