On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Gwamnatin Jihar Kano Ta Fara Tattara Alkaluman Kayuka Da Garuruwa Masu Matsalar Lantarki Domin Magancewa - Injiniya Sani Bala

Gwamnatin Jihar Kano ta ce ta fara aikin tattara alkaluman garuruwa da kayuka da wutar lantarki ba ta kai garesu ba da wadanda ke fama da matsalar wutar domin daukar matakan magancewa.

Shugaban hukumar samar da wutar lantarki a karkara, Injiniya Sani Bala Dambatta ne ya sanar da cigaban a wata zantawa ta musamman da   wakilinmu Nura Haruna Mudi bayan wata ziyara da ya kai kamfanin rarraba hasken lantarki na KEDCO.

Injiniya  Dambatta, yace matakin ya zama wajibi domin cike gibin matsalar lantarki a karkara, Inda ya bada tabbacin cewa bayan kammala tattara alkaluman gwamnatin Engineer Abba Kabir Yusuf za ta samar da mafita.

Haka kuma ya koka akan masu sacewa da lalata kayyakin lantarki wanda ke kawo cikas ga samuwar makamashin a wasu sassan Jihar.

Da yake nasa jawabin Shugaban kamfanin rarraba hasken lantarki na KEDCO Alhaji Ahmed Dangana, ya bayyana damuwa matuka akan masu yin gine-gine karkashin layukan lantarki.

Dangana ya ce a shirye kamfanin ya ke ya hada gwiwa da hukumar samar da lantarki a karkara da sauran hukumomi domin magance matsalolin. sai dai ya bukaci hadin kan al'umma wajen kula da kayyakin lantarki da bada himma wajen biyan kudin wuta.