Gwamnatin jihar Kano tace ta biya naira Milyan 336 a matsayin kudin rijistar jarabawar NECO ta shekarar 2022 ga Dalibai Dubu 29 da 3I.
Kwamishinan Yada Labarai na jihar kano, Malam Muhammad Garba ne ya baiyana haka ga manema Labarai a yau.
Malam Muhammad Garba na wannan bayani ne, bayan fitar wasu rahotanni dake baiyana cewa da yuyuwar Daliban Kano zasu rasa rubuta jarabawar NECO ta shekarar bana, sakamakon gazawar gwamnati wajen biyan kudin jarabawar.
Ya kara da cewa Daliban sun hada da Wadanda suka ci Darussa 9 wanda yawansu ya kama Dubu 15 da 3 13 sai kuma wasu Dalibai Dubu 1 da 18 masu bukata ta musamman da aka biyawa kudin jarabawar.
Kazalika an biyawa wasu Dalibai Mata dubu 7 da 300 ta karkashin shirin tallafawa ilimin ‘ya’ya mata, A yayin a kuma kananan hukumomi suka biyawa Dalibai Dubu 5 da 400.