Gwamnatin jihar Kano ta bayyana damuwarta kan korafin da shugabar kotun sauraron kararrakin zabe ta ‘yan majalisar dokokin a Kano, Mai shari’a Flora Ngozi Azinge ta ce an yi yunkurin bada cin hanci a kotun.
Idan za’a iya tunawa, Azinge ta nuna fushinta kan yunkurin wani babban Lauya mai kwarewar SAN, na ba ta cin hanci.
Ko da yake, ba ta bayyana sunan babban lauyan ba.
Da yake mayar da martani kan alamarin a cikin wata sanarwa, kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Baba Dantiye ya ce gwamnati ta kalli lamarin da matukar damuwa, inda ta dora laifin a kan wasu dakaru masu karfi a cikin jam'iyyar APC.
Ya ce dukkansu a shirye suke su yi amfani da duk wata hanya da za a bi wajen yin adalci kamar yadda aka yi a baya.
Har yanzu dai bangaren APC ba su mayar da martani kan wannan zargi ba har zuwa lokacin gabatar da rahoton a safiyar yau.