Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Bayelsa, BYSEMA, ta gargadi jama’a cewa kayayyakin abincin da wasu mazauna Jihar suka wawashe a wani rumbun ajiya a Yenagoa, babban birnin jihar, bai dace da cin dan Adam ba.
A daren ranar lahadi aka kutsa Gidan ajiyar da ke birnin Yenagoa, wanda akayi amfani da shi wajen ajiye kayayyakin agaji ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a shekarar 2022, insa suka kwashe kayan Baki daya.
Darakta Janar na BYSEMA, Walamam Igrubia, ya shawarci wadanda suka sace kayan da kada su cinye abincin saboda dalilai na lafiya.
Da yake mayar da martani, daya daga cikin mazauna yankin mai suna Alagoa Morris, ya caccaki hukumar ta BYSEMA kan yadda ta kyale kayayyakin da ke cikin rumbun ajiyar suka lalace ba tare da raba su ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a 2022 a jihar ba.