Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari tace tayi nasarar kwato dala biliyan daya da aka sace tun lokacin da aka kafa gwamnatin a watan Mayu na shekarar 2015.
Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami shine ya tabbatar da hakan a ranar Laraba bayan taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya a Abuja.
Sai dai Malami yace an zuba kudiyar da aka kwato zuwa sassa daban-daban na tattalin arzikin musamman domin magance matsalar fatara.
A cewarsa, matakin ya yi tasiri sosai kan matakan yaki da talauci da kuma kawar da matsalolin tattalin arzikin kasa.
Haka kuma Malami bayyana takaici a madadin gwamnati kan cushe da ake samu a kasafin ƙudin Najeriya, ya ce akwai damuwa a tattare da hakan, sai dao za a ɗauki ƙwaƙƙwaran mataki da zasu magance matsalar.