Gwamnatin jihar Legas ta bada umarnin dakatar da dukkanin wasu gine-gine da ake gudanarwa a yankin Banana Island dake birnin na Ikko,Biyo bayan ruguzowar wani bene mai hawa bakwai da ake kan ginawa da aka samu a ranar Larabar data gabata.
Kwamishinan yada labarai na jihar Legas, Gbenga Omotoso ne ya baiyana haka ta cikin wata sanarwa da aka fitar, Ya baiyana cewar an dauki matakin ne, domin tabbatar da jami’an hukumar tsara gine-gine sun gudanar da zuzzurfan bincike a yankin.
Ya kara da cewar matakin zai baiwa gwamnati damar sanin yawan gine-gine da aka yi a yankin batare da samun amincewar gwamnati ba , da kuma zakulo wadanda aka gina su bisa amincewar hukuma.