Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya roki shugaban kasa Muhammadu Buhari, da kada ya bada izinin tafiya hutun karo karatu ga duk wani babban jami’in gwamnati da zai iya kawo cikas wajen rantsar da Bola Tinubu Ahmed Tinubu a matsayin shugaban kasa.
Gwamnan ya bada misali da gwamnan babban bankin Kasa, Godwin Emefiele, wanda ake rade-radin cewar ya nemi izinin tafiya hutun karo karatu daga wajen shugaban kasar, Inda ya bukaci a hana shi.
Matawalle ya yabawa shugaban kasa da uwargidansa kan kokarin ganin an samu sauyi ba tare da wata matsala ba tare da mikawa zababben shugaban kasa, Bola Tinubu mulki cikin salama, sai dai ya koka da yadda wasu jami’an gwamnati ke yiwa shirin zagon kasa.
Gwamnan na zamfara ya zargi gwamnan babban bankin kasa, da aikata lefukan kudi daban daban a kasar nan.
Ya jaddada cewar dole ne gwamnan na CBN ya tsaya gida Najeriya domin yin bayanin duk abin da ya faru a karkashinsa ga gwamnati mai jiran gado.