Gwamnan jihar Taraba Darius Ishaku ya musanta rahotonnin da ke cewa majalisar zartawar jihar ta amince masa da fitar da naira milyan dubu biyu domin saya masa motocin alfarma shi da mataimakinsa da kuma matansu
Mai baiwa gwamnan shawara na musamman kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, Bala Dan-Abu, Ta cikinwata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi ya ce rahoton ba bu kanshin gaskiya a cikinsa.
Ya bayyana rahoton dake cewa majalisar zartaswar jihar ta amince da kudin a matsayin yunkuri na bata sunan gwamnan jihar.
Sai dai jam'iyyar Hamaiyyar ta APP a jihar ta bayyana, amincewa da sayaen motocin alfarma da ake zargin sun kai na naira milyan dubu biyu a matsayin abun ban takaici, a daidai lokacin da ake bin gwamnatin jihar kudaden fansho da na gratiuty.