A cigaba da gaba da nade-naden mukamai da ya ke yi, Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya nada karin wasu mutane 42 a matsayin masu temaka masa da kuma bashi shawara.
Sanarwar da kakakinsa Sanusi Bature ya fitar a daren jiya, Ya ce wadanda aka nada kan mukaman, sun hada da, Yusuf Ibrahim Sharada a matsayin babban mataimakin gwamna kan bangaren fasahar sadarwar zamani.
Kazalika gwamnan ya nada Muhammad Sani Hotoro a matsayin babban mataimakinsa ta bangaren kungiyoyin hadin kai, Sai Barrister Nura Abdullahi Bagwai a matsayin babban mataimakinsa a bangaren shari’a, Sai Hon Surajo Kanawa a matsayin babban mataimakin gwamna ta bangaren wayar da kan jama’a a bangaren Kano ta Kudu.
Shi kuwa Muhammad Sani Salisu Riming ado shine babban babban hadimin gwamna a bangaren wayar da kan jama’a a shiyyar kano ta Arewa, yayin da Nuhu Isa Gawuna zai rike irin wannan matsayi a kano ta tsakiya da sauran mutane daban daban da gwamnan ya nada kan mukamai na siyasa.