Gwamnatin jihar Kano ta fara rabon kayan tallafi da kuma kayan amfanin gona ga masu karamin karfi da mata da kuma manoma da suka fito daga fadin kananan hukumomin jihar kano 44.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya jagoranci kaddamar da rabon kayan tallafin a Hukumar bunkasa aikin gona ta jihar kano, KNARDA da ke karamar hukumar Nasarawa a jiya.
Kayayyakin da za’a raba sun hada da Buhu dubu 297 na Shinkada sai Buhu Dubu Goma na Masara Da Takin zamani Buhu Dubu 2 da 500 da Injinan Feshi da sauran kayan amfanin gonad a kuma Awaki da Tumaki da Raguna har guda dubu 2 da 600.
Gwamna Abba Kabir Yusuf y ace masu bukata ta musamman suma zasu ci gajiyar tallafin , sannan kuma ya yi gargadin cewar duk wani jami’in gwamnati da aka samu da karkatar da tallafin zai ‘dandana kudarsa