Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya sanar da nadin mukaman farko a gwamnatinsa.
Ta cikin wata sanarwa da Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, mukaman sun hadar da Hon. Shehu Wada Sagagi, shugaban Ma’aikata na fadar gwamnati.
Sai Abdullahi Baffa Bichi, sakataren gwamnatin jiha da Dr. Farouq Kurawa sakatare na musamman da Hon. Abdullahi Ibrahim Rogo amatsayin Chief Protocol da kuma Sanusi Bature Dawakin Tofa, Babban Sakataren Yada Labarai.
Wadannan nade-nade sun fara aiki ne daga yau Litinin 29 ga Mayu, 2023.
Sanarwar ta ce an zabi wadanda aka nada ne bisa la’akari da chancanyarsu da sadaukarwa da kuma aminci.