Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo, ya fara hutun kwanaki 21 domin duba lafiyarsa a kasashen waje, inda ya mika ragamar tafiyar da jihar a hannun mataimakinsa, Lucky Aiyedatiwa.
A wasikar da ya aikewa zauren majalisar dokokin jihar da ita, Gwamna Akeredolu, Ya ce mataimaki nasa zai kasance a matsayin mukaddashin gwamna, har zuwa lokacin da hutun da ya dauka na neman lafiya zai kare.
Kakakin majalisar dokokin jihar, Olamide Oladiji wanda ya karfi kwafin wasikar, Ya ce gwamnan zai koma bakin aiki a ranar 6 ga watan gobe.
Ana rika sukar gwamnan sakamakon rashin ganinsa wajen gudanar da aiyukan gwamnati, saboda wata rashin lafiya da yake fama da ita da ba’a baiyana ba, Sai dai hadimansa sun baiyana cewar gwamnan yana cikin koshin lafiya, kafin daga bisani gwamnan ya aikewa majalisar da wannan wasika.