![](https://mmo.aiircdn.com/370/62ea0f0880904.jpg)
Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello Ya bada umarnin rufe daukacin Gidajen masu yawon Ta zubar dake fadin jihar.
Kazalika ya haramta saka Takunkumi a wuraren taruwar jama’ar domin tabbatar da ana gane kowa a jihar. Daukar matakin ya biyo barazanar rashin tsaro da jihar take fuskanta a yan kwanakin nan.
Gwamnan ya bada wannan umarni ne a ranar Talata a birnin Lokoja yayin wani taro da aka shirya kan harkokin tsaro, tare da daukacin masu rike da sarautun gargajiya da kuma shugabannin kananan hukumomi na jihar.
Gwamna Bello ya bada umarnin rushe daukacin wuraren ‘yan kama wuri zauna dake sana’ar yawon Ta zubar a Lokoja da Osara sai Zango da Itobe da Obajana da kuma dukkanin inda suke a jihar.