Gwamnan jihar Bayelsa Douye Diri Ya umarci daukacin zababban shugabannin Kananan Hukumomin jihar da aka rantsar su koma shalkwatar kanana hukumominsu da zama domin yin aiki yadda ya kamata.
Daukar matakin ya biyo bayan halin da mafi akasarin shugabannin kananan hukumomin jihar ke nunawa, inda suke komawa Yenagoa babban birnin jihar da zama.
Da yake jawabi a wajen bukin rantsar da shugabannin Kananan Hukumomin jihar, Gwamna Douye Diri yace manufar bijiro da tsarin shine domin ganin an samu cigaban da ake bukata a daukacin kananan hukumomin jihar.