Gwamnan babban bankin kasa, Godwin Emefiele, ya roki ministan kwadago, Chris Ngige, da ya temaka ya dakile yunkurin shugabancin kungiyar kwadago ta kasa NLC kan zanga-zangar da ta shirya gudanarwa a ranar Laraba.
Idan za a iya tunawa dai a ranar Juma’ar da ta gabata ne, shugabannin kungiyar ta NLC suka baiyana cewar zasu rufe daukacin rassan bankin a fadin kasar saboda karancin kudi da ake fama da shi a Najeriya.
Sai dai a wata ganawar sirri da aka yi a ma’aikatar kwadago da ke Abuja a ranar Litinin, Emefiele ya ce zanga-zangar za ta kawo cikas ga ci gaban babban bankin idan ba a dakile tab a.
A yayin ganawar akwai Shugaban kungiyar kwadago Joe Ajaero yayin da Emefiele ya jagoranci jami’an babban bankin zuwa taron wanda Ministan ya jagoranci ganawar.
Har zuwa wannan lokaci babu wata sanarwa a hukumance da aka fitar kan ko an cimma wata matsaya ko kuma akasin haka.