Gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike yayi alkawarin kara rubunya harkokokin siyasarsa daga jiharsa gabanin babban zaben kasar nan mai zuwa, inda ya baiyana cewa dabarun da zai yi amfani zasu bawa abokan hamaiyyarsa mamaki.
Gwamna ya baiyana haka ne yayin kaddamar da rukunin gidaje na majalisar dokokin jihar a birnin Fatakwal, Wike yace zai mayar da hankali ne a wajen samar da aiyukan raya kasa domin amfanar dimokradiyya ga al’ummar jihar.
Wasu rahotanni dai sun baiyana cewa gwamnan ya cire tutar jam’iyyar PDP daga fadar gwamnatin jihar Ribas sannan kuma ya kai karar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar da kuma gwamnan jihar Sokoto bisa takaddamar tikitin takarar shugaban kasa.
Sai dai gwamna wike ya baiyana labarin a matsayin wani aiki na masu hamaiyya dashi, inda yayi alkawarin fara yin siyasar a aikace a lokacin da ya kammala gabatar da jerin aiyukan raya kasa.